Kungiyar ISWAP Mai Ikirarin yin Jihadi A Yammacin nahiyar Afrika, Ta dauki alhakin harin da aka kai gidan gyaran hali na kuje dake birnin Taraiyya Abuja a ranar Talata.
Bayanin hakan na a cikin wata sanarwa da kungiyar ta wallafa da harshen Larabci a shafinta na Amaq dake kan internet.
A yayin da Hukumomin kasar nan suka alakanta harin da ‘Yan Ta’adda, A yanzu haka Mayakan Boko Haram 64 cikinsu hadda Kwamandojinsu 15 wadanda suka kitsa harin da aka kai kan jirgin kasa a jihar Kaduna, a ranar 28 ga watan Maris din Bana, suna daga cikin wadanda suka arce daga gidan gyaran halin.
A yayin da al’umma ke tsaka da yin tir da harin da aka akai, A jiya ne shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci gidan gyaran halin domin ganin yadda harin ya kasance.
Bayan anyi masa bayanin abunda ya faru, Shugaban Kasar ya nuna bacin ransa ga jami’an tsaro na sirri dake gidan gyaran halin wanda yace akwai dimbin ayar tambaya akansu.