Kungiyar malaman kwalejojin ilimi ta kasa COEASU, Ta koka kan yadda aka tsame ‘ya’yan daga cikin wadanda gwamnatin taraiyya ta yiwa karin albashi da kaso 40 bisa 100.
A sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Laraba, Ta baiyana matakin tsame ta da kuma sauran wasu ma’aikatan manyan makarantu daga tsarin a matsayin wani shiri na haddasa rudani.
Bugu da kari ta baiyana matakin a matsayin wani salo na nuna wariya tare da kokarin raba kan ma’aikatan kasar nan, ta yadda ba zasu iya magana da murya daya ba kan abubuwan da ya shafi jin dadinsu.
Kungiyar ta COESU, Ta ce rabon da gwamnatin taraiyya ta yi mata karin albashi tun shekarar 2010 , wanda ya kama shekara 13 ke nan.