Kungiyar malamai ta kaa ta roki gwamnatin taraiyya data gaggauta aiwatar da sabon tsarin albashi da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince dashi a shekarar 2021.
Shugaban kungiyar na kasa, Audu Titus ne ya baiyana haka a ranar Laraba, lokacin da yake ganawa da wakiliyarmu Joy Eberebe, dangane da ranar Malamai ta bana, wadda aka yiwa take da, Cigaban Ilimi yana somawa ne daga Malamai.
A cewarsa sabon tsarin albashin malamai da shugaban kasa muhammadu Buhari ya amince dashi a yayin bukin ranar Malamai ta bara, har yanzu ba’a fara aiki dashi ba a matakin jihohi da kuma taraiyya.
Shugaban kungiyar Malaman ta kasa ya baiyana cewa amincewa da sabon tsarin albashin da kuma inganta walwalarsu zai temaka wajen bunkasa kwazonsu.