Yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da ma'akatan sufurin jiragen sama na kasa suka fara yi ya zo karshe, bayan rokon da suka ce wasu 'yan Najeriya masu kishin kasa sun yi musu
Kungiyar Ma’aikatan Sufurin jiragen sama dake filin jirgin saman Malam Aminu Kano, Sun janye yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki 2 da suka yi.
A shekaran jiya ne, Kungiyar Wadda ke a karkashin hadaddiyar kungiyar Ma’aikatan Sufurin jiragen sama ta kasa, ta gudanar da wata zanga-zanga bisa zargin gwamnatin Taraiyya wajen gaza aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla, da kuma rashin aiwatar da sabon mafi karancin Albashi kafin su fara yajin aikin gargadin.
Matakin da suka dauka ya gurgunta yanayin gudnaar da aiyuka a Hukumar kula da Sararin samaniya ta kasa NAMA da kuma Hukumar Kula da Yanayi ta kasa, NiMet, sai kuma Hukumar Kula da Sufurin Jiragen sama ta kasa NCAA.
A zantawarsa da wakilinmu Victor Chiristopher, Wakilan Kungiyar ta kasa dake a nan kano, a karkashin kwamared Akubo Benjamin, wanda Abdullahi Ibrahim Yayi magana a madadinsa, Yace sun janye yajin aikin ne biyo bayan rokon da wasu ‘yan Najeriya masu kishin kasa suka yi masu, sakamakon rashin jin dadin abubuwan da yajin aikin ya haifar.
Kazalika shima shugaban kungiyar Kwararrun Ma’aikatan Sufurin jiragen sama ta kasa ANAP reshen jihar Kano, Kwamared Isa Aliyu, Yayi barazanar cewar kungiyar zata dauki matakin tafiya yajin aikin sai Baba ta gani muddin gwamnatin taraiyya ta gaza biya masu bukatunsu.