Janyewar ta biyo bayan ganawar da suka yi tsakaninsu da ministan kwadago da samar guraban aikin yi, Dr Chiris Ngige a jiya.
Sanarwar da shugaban Sashin Hulda da jama’a da kuma Yada Labarai na Ma’aikatar kwadago ta kasa ya fitar , Ya baiyana cewa an kafa wani kwamiti wanda zai yi duba na tsanaki kan bukatun da kungiyar Ma’aikatan Lantarkin ta kasa domin warware su cikin salama.
Da yake tabbatar da janye yajin aikin a daren jiya, Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Lantarki ta kasa, Kwamared Joe Ajero, Yace zasu dakatar da yajin aikin nasu nan da tsawon makwanni biyu kamar yadda suka kulla yarjejeniya tsakaninsu da gwamnatin domin biya masu bukatunsu.
Kazalika yayi fatan gwamnatin taraiyya zata yi adalci kan matsalolin da suka Dade suna ci masu tuwo a kwarya domin magance su.