On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kungiyar Likitoci Ta Zargi Ministar Kudi Da Kin Sakar Masu Kudaden Alawus Na Yin Aiyuka Masu Hadari

TAMBARIN KUNGIYAR LIKITOCI MASU NEMAN KWAREWA

Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta kasa ta zargi Ma’aikatar kudi ta kasa da kin biyansu sabon karin kudaden alawus na yin aiyuka masu hadari wanda gwamnatin taraiyya ta amince a biya su.

Shugaban kungiyar na kasa, Dr. Dare Ishaya ne ya baiyana haka yayin ganawarsa da manema Labarai, Yace tuni aka ware kudaden, amma  ma’aikatar kudi ta taraiyya tayi ‘keme-me wajen kin sakin kudin.

A watan Disambar bara ne, aka yiwa Ma’aikatan Lafiya da kuma Likitoci karin kudaden alawus na shiga aiyuka masu hadari, domin ganin an inganta aiyukansu.

To sai dai shugaban  kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta kasa, Yace yanzu ma’aikatar kudi ta kasa bata saki kudin ba, a yayin da duk wani kokari da yayi domin  ganin minister kudin Zainabr Ahmed Shamsuna yaci tura.