Kungiyar likitocin ta kasa NMA reshen jihar Plato ta nesanta kanta daga alaka da Dr Noah Kekere, wanda aka kama bisa zargin satar kodar wata mata.
Idan dai za a iya tunawa, ‘yan sanda sun kama wanda ake zargin ne a garin Jos bayan wani dan kasuwa, Alhaji Kamal, ya zarge shi da cire kodar matarsa a lokacin da aka yi ma ta tiyata a shekarar 2018.
Da yake mayar da martani, shugaban kungiyar NMA a jihar, Dr Bapigaan William Audu, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce a binciken da suka yi kan al’amarin, ya nuna cewa Kekere ba likita ba ne.
A cewar sanarwar, binciken kwakwaf da kungiyar ta yi, ya nuna cewa shi mutum ne mai kwarjini da ke sojan gonad a nuna cewa shi likita ne.