Kungiyar Kwadago ta kasa ta shirya domin gudanar da wata gagarumar zanga-zanga ta tsawon kwanaki biyu a fadin kasar nan, daga ranar 26 zuwa 27 ga watan da muke ciki, a wani mataki na nuna goyon baya ga yajin aikin da malaman jami’oin kasar nan da sauran wasu kungiyoyi dake makarantun gwamnati ke yi a halin yanzu.
Wata sanarwa dauke dasa hannun shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Ayuba Wabba, da Kuma Babban Sakataren Kungiyar na kasa, Emmanuel Ugboaja, Tace za’a yi zanga-zangar ne a daukacin jihohin kasar nan, cikinsu hadda Abuja babban birnin taraiyya.
Bugu da kari sanarwar ta baiyana cewa, Za’a fara zanga-zangar ne daga daukacin shalkwatocin kungiyar kwadago na jihohi, yayin da Abuja zanga-zangar zata soma daga sakatariyar kungiyar kwadago ta kasa.
A wani bangaren kuma, Mai magana da yawun rundunar yansanda ta kasa, Muyiwa Adejobi ya shawarci wadanda ke shirin gudanar da zanga-zangar dasu sanar da jami’an yansanda, domin ganin an samar masu da tsaro a lokacin da zasu yi zanga-zangar.
A wani bangaren kuma,Hadaddiyar Kungiyar Ma’aikatan Banki Masu Harkokin Inshora da al’amuran tafiyar da kudi ta kasa, Sunce zasu bi sahun kungiyar kwadago ta kasa wajen gudanar da zanga-zangar lumana ta tsawon kwanaki biyu, domin nuna rashin jin dadinsu game da dogon yajin aikin da kungiyar Malaman jami’oi ta kasa ke kan yi.
A cikin wata sanarwa mai dauke dasa hannun shugaban kungiyar na kasa Anthony Abakpa da kuma babban Sakataren kungiyar Mohammed Sheik, wadda aka fitar a ranar Lahadi, Tace Yajin aikin wanda aka fara tun ranar 14 ga watan Fabarairun bana yakai ma’kura, wanda hakan yasa yake cigaba da gurgunta kwazon dalibai da haddasa wasu matsaloli.
Daga nan kungiyar tayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, daya yayi abunda ya kamata domin ganin an kawo karshen yajin aikin da kungiyar ta ASUU ke yi.