Kungiyar Kwadago ta ta caccaki hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa kan yadda ake rufa-rufa wajen biyan kudaden tallafin mai a kasar nan.
Kungiyar ta NLC ta kuma yi zargin cewa tsarin cike yake da almundahana, kamar yadda ta rubuta takardar kokenta ga kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai da aka domin yin bincike kan yadda ake biyan kudaden tallafin man.
Takardar mai dauke dasa hannun Shugaban kungiyar kwadago ta NLC na kasa, kwamaren Ayuba Wabba, ta yi imanin cewa daya daga cikin manyan dalilan da ke haifar da karuwar farashin man fetur a kasar nan lokaci zuwa lokaci, nada nasaba da yadda sai gwamnati ta shigo da Tacaccen Mai da jama’a zasu yi amfani dashi.
Kungiyar ta kara da cewa, Al’umma da dama suna tabbacin cewa cire tallafin mai ga man da ake shigo dashi cikin kasar nan shine mafita, ta bangaren bunkasa cigaba a kasar nan.