Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta koka kan karin farashin man fetur tsakanin naira dubu 1 da 50 zuwa Naira dubu 1 da 150 kan kowace lita da aka yi a baya-bayan nan, inda ta bayyana hakan a matsayin kololuwar rashin adalci ga talakawa.
Mataimakin shugaban kungiyar ta NLC, Farfesa Theophilus Ndubuaku ne ya bayyana haka a jiya, inda ya ce , kamata ya yi ayi zama na musamman da kungiyoyi masu zaman kansu da dalibai domin tattaunawa kan matakin da za a dauka kafin daukar wannan mataki.
Ya shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da ya yi amfani da irin salon da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ke amfani da shi, inda yake shirya taron tattaunawa na wata-wata tare da masu ruwa da tsaki a kan wasu muhimman batutuwa da ke da alaka da jin dadin ma’aikata.
Hakan dai na zuwa ne a yayin da ‘yan kasuwar man fetir suka musanta zargin da ake yi musu na zama masu hannu a tashin farashin man fetur din da aka samu a fadin kasar nan.