Kungiyar Kwadago ta kalubalanci shirin da gwamnatin tarayya ke yi sake fasalin kamfanin samar da hasken wutar lantarki na kasa.
Idan za a iya tunawa, Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar kula da Kamfanonin Gwamnati ta bayyana shirin sayar da kashi 40 na hannun jarin gwamnati a kamfanonin rarraba wutar lantarki a kasuwar hada-hadar jari ta kasa a sabuwar shekara ta 2024.
A cikin wata takardar bayan taro da shugaban kungiyar kwadago ta kasa kwamared Joe Ajaero ya fitar a ranar Talata, ya ce ‘yan Najeriya sun sha jin irin wannan labarin tsawon shekaru da suka gabata, ba tare da ganin wani kyakykywan sakamako ba, bayan an cefanar da kadarorin gwamnati saima karin wahalhalu da tsarin ke janyo wa al’ummar Najeriya da tattalin arzikin kasa.
Ya bayyana cewa dalilin da ya sa ake shirin sake fasalin kanfanin samar da hasken lantarkin na kasa TCN, nada alaka da ganin an baiwa wasu manyan masu rike da madafun iko,a kasar nan damar karbe ikon tafiyar da harkokin lantarkin a Najeriya domin suci karensu ba bu babbaka.