Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta yi Allah wadai da shawarar da gwamnonin jihohi suka bayar na neman gwamnatin tarayya ta kori ma’aikatan da suka haura shekara 50 tare da sanya haraji kan ‘yan Najeriya da suke da kudi sama da naira Dubu 30.
Domin shawo kan tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan, gwamnonin sun bayar da shawarar cire tallafin man fetur.
Kazalika an ce sun roki Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da bashin da ake bin kasar nan na Naira Tiriliyan 19 zuwa tsarin biyan bashi ta hanyar tsarin hannun jari wanda zai dauki tsawon shekaru 100, sannan kuma ya rage ayyukan da Kamfanin Mai na kasa ke gudanarwa da kuma rage ayyukan mazabu da ‘yan majalisa ke gudanarwa da sauransu.
To sai dai shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC, kwamared Ayuba Wabba, ta cikin wata wasika da ya aike wa shugaban kasa mai kwanan wata 8 ga watan Agustan da muke ciki, ya ce shawarar da gwamnonin suka gabatar tsantsar son kai ne da rashin sanin ya kamata tare da rashin yin duba kan halin da mutanen kasa suke a ciki.