Kungiyar kwadago ta NLC da takwararta ta TUC sun janye aniyarsu ta tafiya yajin aiki daga yau Laraba, domin nuna bacin ransu kan karancin takardun naira da ake samu a kasar nan.
Kungiyoyin biyu sun baiyana cewar zasu cigaba da saka ido kan wadatuwar takardun kudin da aka samu a bankunan kasuwanci, kamar yadda babban bankin kasa ya bada tabbacin samuwar kudin,kafin nan da makwanni biyu masu zuwa domin sanin mataki na gaba da zata dauka.
Shugaban kungiyar kwadago ta NLC Joe Ajaero da takwaransa na TUC Festus Osifo ne suka baiyana haka yayin wani taron manema Labarai na hadin gwiwa da aka shirya a ranar Talata a Abuja, jim kadan bayan kammala taron kwamitin kolin kungiyoyin na kasa.
Sun baiyana cewar bayan jawabin da suka samu daga majalisun kungiyoyin na jihohi 36 da kuma birnin taraiyya Abuja, Kungiyoyin kwadagon sun cimma matsayar janye umarnin da suka fara baiwa ma’aikata na yin zaman dirshan a gidajensu.