Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun gindaya wadansu sharudda akan batun sake sake duba mafi karancin albashi na kasa.
Kungiyoyin sun baiyana cewa, sun dauki matakin ne la’akari da yadda hauhawar farashin kayayyaki ke ci gaba da yin ‘kamari, da kuma faduwar darajar Naira wanda dole ne a yi la’akari dasu, kafin yin wata magana ta karin albashin da gwamnatin tarayya ta sanar.
Kungiyar kwadagon ta bayyana cewa kusan duk farashin wani kayan masarufi da ake amfani dashi a kasar nan ya tashi, inda ta baiyana cewa muddin aka cigaba da tafiya a haka, to babu wani karin albashi da zai gamsar da ma’aikatar kasar nan.
Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun baiyana haka ne a matsayin martani ga kalaman da Ministan Kwadago da nagartar aiki Chris Ngige ya yi, inda ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba Gwamnatin Tarayya za ta bayyana karin albashi ga ma’aikatan gwamnati saboda karuwar farashin kayayyakin masarufi.