Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta sake jaddada matsayar cewar babu gudu ko ja da baya, kan matakin da zata dauka, na umartar ma’aikatan kasar nan su kauracewa bakin aiki, muddin gwamnatin taraiyya ta gaza kawo karshen matsalar karancin takardun kudi da Man fetir nan da kwanaki bakwai masu zuwa.
Bayanin hakan na kunshe ne ta cikin wata takardar bayan taro da kungiyar ta fitar a ranar Talata, Jim kadan bayan kammala taron kaddamar da kwamitin kolin kungiyar da aka yi ranar Litinin a Abuja.
Idan ba’a manta ba, Shugaban kungiyar kwadagon ta kasa Joe Ajaero, ya fitar da sanarwar barazanar tafiya yajin aiki na fadin kasa, inda kuma ba’a jima ba ,babban bankin kasa CBN, Ya umarci daukacin bankunan kasar nan dasu fara karba da kumabayar da tsohon kudi.
To sai dai duk da wannan sabon cigaba da aka samu, Kungiyar kwadagon ta cikin wata sanarwa data fitar, t ace har yanzu tana kan bakanta na umartar ma’aikata su tafi yajin aiki, Matukar gwamnatin taraiyya bata kawo karshen matsalar karancin takardun kudi nan da kwanaki bakwai masu zuwa ba.