On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Kungiyar Kwadago NLC Ta Bukaci Gwamnatin Najeriya Ta Rage Kudin Lasisin Kafafen Yada Labarai

Kungiyar Kwadago ta kasa NLC ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta rage kudin sabunta lasisin kafafen yada labarai a kasarnan saboda tabarbarewar tattalin arziki da ake ciki.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Ayuba Wabba, ya fitar a Abuja.

Kamfanin dillancin labaru na kasa NAN ya ruwaito cewa, wannan kiran ya zo ne a daidai lokacin da hukumar NBC ta sanar da mahukuntan kafafen yada labarai 52 matakin janye lasisin su saboda rashin biyan kudin  sabunta lasisi.

A  ranar 20 ga watan Agusta da muke ciki hukumar NBC ta kara wa’adi ga dukkanin kafafen yada labarai da abin ya shafa su biya basussukan da ake binsu kafin ranar 23 ga watan na Agusta.