Kungiyar kwadago ta kasa ta ce za ta fara yajin aikin gama gari a fadin kasarnan daga ranar 14 ga watan Agusta na 2023 da muke ciki, idan ma’aikatar shari’a ta tarayya ta gaza janye karar da ta shigar a kan kungiyar.
NLC ta yanke wannan shawarar ne a yayin taronta na majalisar zartarwa ta kasa wanda aka gudanar a Abuja, ranar Alhamis.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa mai dauke da sa hannun shugaban NLC da kuma sakataren kungiyar, Joe Ajaero da Emmanuel Ugboaja.
Sunce ma'aikatar shari'a da kotun ma’aikata ta kasa sun ci gaba da ba da damar yin amfani da su a matsayin wakilan makiya Dimukuradiyya.