Kungiyar kwadago a Najeriya ta sake gargadin cewa mambobinta za su fara yajin aikin a fadin kasarnan ba tare da wata sanarwa ba idan ‘yan kasuwar suka kara farashin man fetur ba tare da kammala tattaunawar da ake yi ba.
Shugaban NLC, Joe Ajaero, yayin da yake tabbatar da hakan a ranar Litinin, ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta dakatar da matsalar faduwar darajar Naira.
Da yake jawabi a taron kungiyar kwadago ta Afirka da ke gudana a Abuja, Ajaero ya shawarci gwamnatin tarayya da ta canza munanan manufofin tattalin arziki da ke sanya albashin ma’aikata na tashi ba’a bakin komai ba.
Barazanar da kungiyoyin kwadagon suka yi ta biyo bayan rade-radin da akeyi cewa ‘yan kasuwar man fetur, na iya kra kudin litar mai zuwa 720 a makonni masu zuwa idan dala ta ci gaba da tashi zuwa 950.