Ana cigaba da martani akan karin farashin man fetur daga Naira 540 zuwa Naira 617 kowace lita a Najeriya, yayinda ma’ajin kungiyar kwadago ta kasa NLC, Hakeem Ambali ya fadawa manema labarai cewa kungiyar za ta kira taron majalisar zartarwarta na kasa biyo bayan karin farashin.
Da yake magana a gidan talabijin, shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC, Joe Ajaero, ya ce ana yaudarar ‘yan Najeriya kan batun farashin man fetur.
Tun da farko, shugaban kungiyar kwadago ta kasa a jihar Rivers, Alex Agwanwor, ya shaidawa gidan Radiyon Nigeria Info cewa kungiyar zata shirya yajin aikin a fadin kasarnan saboda sabon farashin man fetur.
Har ila yau, jam'iyyar PDP ta bayyana karin farashin man fetur na baya-bayan nan amatsayin tunzura ‘yan kasa da kuma gayyatar rikici a fadin kasarnan.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba a cikin wata sanarwa da ya fitar, yace tsarin farashin man Fetur a halin yanzu tsantsar rashin tausayi ne, yana mai zargin cewa gwamnati na son mutanen da suka Tagaiyyara saboda tsananin wahala.