Kungiyar Yan Aware ta yankin Kudu maso gabashin kasar nan da aka fi sani da IPOB, Ta nuna bacin ranta kan jan kafar da Kotun Kolin kasar nan ke yi, dangane da daukaka karar da gwamnatin taraiyya ta yi,kan kalubalantar hukuncin da Kotun daukaka kara ta yi na wanke jagoransu, Mazi Nnamdi Kanu.
A wata sanarwa da kakakin kungiyar Emma Powerful ya fitar, Ya ce jinkirin gudanar da shari’ar da ake samu abun damuwa ne.
Kungiyar ta IPOB ta baiyana mamakinta kan yadda Kotun Kolin zata buge da sauraren kararrakin da suka shafi ‘yan siyasa,amma kuma take nuna halin ko in kula akan shari’ar jagoran nasu.
Daga karshe kungiyar ta zargi Kotun kolin kasar nan da nuna son kai cikin al’amuranta.