Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya zargi Kungiyar ‘Yan Aware ta IPOB da laifin fasa bututan Mai da Sauran kayayyakin amfanin Yau da Kullum.
A yayin hirarsa da jaridar Bloomberg, Shugaba Buhari ya koka kan yadda lefukan da kungiyar ke aikatawa suka kawo nakasu wajen aiyukan hako albarkatun mai a kasar nan, Sai dai kuma yace an dauki dukkanin wasu matakai da suka dace domin dakile lefukan satar Danyen Mai da kuma Fasa Bututan Mai.
Kazalika yace, A Bara gwamnatinsa ta fara yunkurin cire tallafin Mai, amma daga bisani ta gano cewa yunkurin bai dace ba.
Da yake mayar da martani game da zargin da aka yiwa Kungiyar ta IPOB, Sakataren Yada Labaranta, Emma Powerful, Ya baiyana ikirarin da shugaban kasar yayi a matsayin abun dariya, Inda ya jaddada cewa abunda kungiyar tasa gaba shine tabbatar da samun yancin kasar Biyafara, Ba wani abu can na daban ba.