Wata kungiyar kungiyar farar hula mai suna FIDA, ta bukaci gwamnatin jihar Kano data aiyana dokar ta baci a bangaren samar da ruwan sha a jihar Kano.
Kungiyar ta yi kira ga gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf da ya gaggauta amincewa da fitar da kudi domin magance matsalar karancin ruwan sha da ake fuskanta.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar Dr. Abdussalam Muhammad Kani ya fitar a jiya, Ya bukaci gwamnatin jihar kano data gyara daukacin kayayyakin samar da ruwa da ake das u domin samar da wadatuwarsa a birni da karkara.
Idan ba’a manta ba a kwanan nan ne Hukumar samar da ruwan sha ta jihar kano ta yi karin haske kan dalilan da suka sabbaba matsalar karancin ruwan sha, wanda ta ce yana da alaka da gyare-gyaren da ake yi a challawa da Tamburawa, A yayin da ‘yan garuwa suka kara kudin ruwa daga naira 50 zuwa 150 akan kowacce jarka daya a sassa daban daban na kwaryar birnin kano.