An kammala babban taron na musamman kan al'amuran siyasa a Jamhuriyar Nijar a Abuja tare da bada umarni ga hafsoshin tsaro na ECOWAS da su fara aiki tare da tura rundunoni da dukkan bangarorinsu domin dawo da tsarin mulki a kasar.
Da yake karanta sanarwar taron shugaban hukumar ECOWAS, Omar Alieu Toura, ya yi kira ga kungiyar tarayyar Afrika da dukkan kasashe da hukumomin da ke kawance da su, ciki har da Majalisar Dinkin Duniya da su amince da duk wasu kudirorin da hukumar ta dauka domin tabbatar da ganin an dawo da tsarin mulki a Nijar cikin gaggawa.
Taron ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da maido da tsarin mulkin kasar.
Toura ya ce an dauki wadannan kudurori ne bayan da aka yi nazari sosai kan rahotannin wakilai daban-daban da aka aika domin tattaunawa da gwamnatin mulkin soja a Nijar.