Kungiyar Dattawan Arewa tayi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya dage takunkumin tattalin arziki da aka kakabawa Jamhuriyar Nijar.
Shugaban kungiyar ta Ango Abdullahi, ya bayyana damuwarsa kan yadda ake amfani da karfi wajen maido da tsarin mulkin jamhuriyar Nijar, yana mai cewa da wuya a samu sakamako mai kyau.
Ya kuma jaddada cewa cire takunkumin zai taimaka wajen gudanar da shawarwari, don haka ya bukaci yin aiki da diflomasiyya.
Idan dai za a iya tunawa kungiyar ECOWAS karkashin jagorancin Tinubu ta sanya takunkumin hana wutar lantarki da kuma rufe kan iyakokin Nijar jim kadan bayan hambarar da zababben shugaban kasar Mohammed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli.