Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta yi barazanar cewa za ta tsayar da dukkanin wasu ayyuka a fadin kasar nan, idan har gwamnatin tarayya ba ta janye karin kudaden karatu na manyan makarantu ba.
Shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Usman Barambu shi ne ya yi wannan barazanar a ranar Alhamis yayin da yake jawabi a wani taron da aka gudanar a kwalejin kimiyya da fasaha ta Abubakar Tatari Ali da ke jihar Bauchi.
Ya ce karin kudin makaranta ya yi illa ga yawancin daliban da ke makarantun gaba da sakandare.
Shugaban kungiyar ta NANS ya yi gargadin cewa idan har Gwamnatin Tarayya ba ta gaggauta janye matakin ba, kungiyar za ta zaburar da daukacin daliban manyan makarantun kasar nan domin gurgunta duk wasu harkokin gudanar da aiyukan gwamnati a Najeriya.