Gwamnatin tarayya ta cire manyan makarantun kasar nan daga cikin tsarin na biyan albashin bai daya mai taken (IPPIS) ba tare da bata wani lokaci ba.
Haka kuma an umurci Jami’o’in kasar nan da su fara daukar ma’aikatan da suke bukata, ba tare da neman wani izini daga ofishin shugabar ma’aikata ta kasa ba, domin a rage yawan wahalhalun da ake fuskanta a bangaren ilimi.
Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka a karshen taron majalisar zartarwa na kasa da aka gudanar jiya a Abuja, inda ya ce an dauki matakin ne domin rage kalubalen da ke fuskantar manyan makarantun kasar nan.
A wani bangaren kuma, , Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa, taron majalisar zartarwa na kasa ya amince da sake duba bangarorin da hukumar hana fasa kwauri ta kasa ta daukewa biyan haraji, domin magance matsalar zurarewar kudaden shiga da ake samu.
Nan kuma, kungiyar dalibai ta kasa NANS, ta yabawa gwamnatin tarayya bisa yadda ta cire manyan makarantun kasar nan da ga cikin tsarin biyan albashi na IPPIS.
Kungiyar ta ce matakin zai kawo karshen wani bangare na rashin jituwa da ake yawan samu daga bangarorin.
A wata sanarwa da shugaban majalisar kolin kungiyar na kasa, Kwamared Akinteye Afeez ya fitar a daren jiya, ya ce matakin zai saukaka yanayin gudanar da al’amura a makarantun kasar nan.