Kungiyar Dalibai ta kasa NANS na shirin tattaunawa da Ministan Kwadago Chris Ngige da Ministan Ilimi, Adamu Adamu kan rahotannin zargin Gwamnatin Tarayya ba ta da kudin da za ta biya bukatun Kungiyar Malaman kungiyar Jami'oi ASUU da ke yajin aiki.
Sai dai kungiyar daliban ta nesanta kanta da wani rahoto na neman korar gwamnan babban bankin kasa CBN Godwin Emefiele da wasu dalibai suka yi.
Mataimakin shugaban kungiyar, Odiahi Ikhine, ya nunar da cewa daliban ba su ji da din kalaman karamin ministan kwadago Festus Keyamo ba, cewa gwamnati ba ta da kudin biyan bukatun ASUU.
Ikhine ya ce shugabannin kungiyar za su gana da Adamu da Ngige bayan shugaba Buhari ya ba da umarnin a warware yajin aikin cikin makonni biyu yayin da ya kuma sha alwashin ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an yi abin da ya dace.