Kungiyar kiristoci ta kasa CAN ta gargadi gwamnatin tarayya kan tattaunawa da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ko kuma yi musu afuwa.
Kungiyar ta ce idan har gwamnatin Tarayya ta kasance ba ta da wani takabus kuma ba za ta iya yakar ta’addanci ba, ya kamata ta nemi taimako daga kasashen waje.
Sakataren kungiyar CAN shiyyar Arewa maso Yamma Sunday Oibe ne ya yi wannan gargadin a karshen mako, yayin da yake mayar da martani kan zargin wasu jami’an gwamnatin tarayya na tattaunawa da ‘yan bindiga a jihar Zamfara.
Ya dage cewa tattaunawa ba ita ce mafita ba, a maimakon haka, nuna azama da kishin kasa irin na siyasa zai taimaka wajen kawar da masu laifi daga tushe.