Wata sabuwa na neman kara kunno kai a Jami’oin kasar nan, A yayin da kungiyar Malaman jami’oi ta kasa ke shirin yin wani taron gaggawa na kwamitin kolin kungiyar na kasa.
Duk da cewar ba’a saka ranar da za’a gudanar da taron ba, rahotanni na baiyana cewa, daukar matakin ya biyo bayan yadda, aka turawa ‘Yayan kungiyar Malaman jami’oin ta kasa rabin albashinsu na watan Oktoban da ya gabata.
Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Emmanuel Osodoke ya tabbatar da cewar ba’a turawa malaman cikakken albashi ba, a yayin ganawarsa da manema Labarai a Abuja.