Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa ASUU ta yi watsi da shirin da Asusun Tallafawa Manyan Makarantu na kasa TETFund ke yi na sanya jami’o’i masu zaman kansu a matsayin wadanda za su ci gajiyar ayyukansa.
Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana haka a taron kwana biyu na tattaunawa tsakanin TETFund da daukacin kungiyoyi a Abuja ranar Laraba.
Osodeke ya ce matakin shigar da jami'o'i masu zaman kansu a cikin aikin asusun zai haifar da yaduwar jami'o'i masu zaman kansu marasa inganci.
Ya bukaci asusun da ya kara yin aiki tsarin sa ido kan ayyukan makarantun yana mai cewa matakin gudanar da ayyukan bai dace ba saboda suna karbar makudan kudade.