Majalisar Wakilai taga baiken shugaban kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, bisa ikirarin da yayi na cewar, kakakin zauren majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila , ya yaudari malaman jami’oin kasar nan, bayan da yayi uwa da makarbiya wajen ganin sun janye yajin aikin watanni takwas da suka dauki lokaci suna yi.
A wata sanarwa da shugaban kwamitin yada labarai da hulda da jama’a na majalisar, Benjamin Kalu ya fitar a jiya, Yana mai cewa babu wani lokaci da aka cimma wata matsaya tsakanin malaman jami’oin da kuma kakakin majalisar akan cewar za’a biyasu albashin su na lokacin da suka dauka suna yajin aiki.
Sai dai kuma, a hirarsa da manema Labarai, Shugaban Kungiyar ASUU ya jaddada cewar, kungiyar ta janye yajin aikin ta a ranar 14 ga watan October ne a sakamakon alkawuran da kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila yayi masu na cewar za’a biya su hakkokinsu.