Kungiyar Malaman Makarantun Fasaha ta ASUP, ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya rattaba hannu a kan dokar da za ta soke bambancin dake tsakanin shaidar digiri ta BSC da HND kafin ya bar mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
Shugaban kungiyar ASUP na kasa, Kwamared Anderson Ezeibe, wanda ya yi wannan kiran a wata zantawa da jaridar Vanguard jiya a Abuja, ya ce matsalar ta sanya matasan Najeriya ba sa sha’awar ilimin kimiyya da kere-kere a kasar nan.
Ya ce zai zama abin tarihi idan shugaba Buhari ya amince da kudurin ya zama doka kafin ya bar mulki.
Kudurin dokar dake neman kawar da nuna wariya ga daliban da suka kammala karatun HND da takwarorinsu na jami’o’i a fannin aiki da karin girma a wuraren aiki ya samu amincewar majalissun dokoki tun shekarar 2021.