Shekaru hamsin da uku bayan yakin basasar Najeriya, majalisar wakilai ta yi karatu na uku, ga kudirin kafa hukumar raya kudu maso gabas.
Majalisar dai ta dauki wannan matakin ne a gaban kwamitin da mataimakin kakakin majalisar Rt. Hon. Benjamin Okezie Kalu ke jagoranta bayan nazarin rahoton kudirin.
Kudirin ya bayyana cewa za a ɗora wa hukumar alhakin karɓa da sarrafa kudade daga rabon asusun tarayya.
Asusun dai an yi shi ne domin sake gina tituna da gidaje da sauran barnar ababen more rayuwa da yankin ya fuskanta a sakamakon yakin basasa da kuma magance matsalolin muhalli.