Bankin duniya ya baiyana cewar takardar naira ta nan gida Najeriya na cikin sahun jerin kudi mafi lalacewa a nahiyar Afrika.
Bankin ya baiyana cewar darajar kudin Najeriya ta sauka da kimanin kaso 40 bisa 100 akan takardun kudi na Dala a tsakiyar watan Yunin bana.
Bankin ya tabbatar da haka ne ta cikin rahotonsa na mahangar tattalin arzikin kasashen Afrika na wannan watan da ya fitar.
Rahoton ya alakanta raunin takardar naira da ake fuskanta da matakin da babban bankin kasa ya dauka na janye takunkumin da yasa a bangaren musayar kudaden kasashen ketare a hukumance.