Kotun Koli ta shigar da karin jihohi tara a matsayin masu shigar da kara akan Karar da gwamnatocin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara ke kalubalantar wa'adin chanjin takardun kudi na Naira.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamna Nasir El-Rufai da Yahaya Bello na Kaduna da Kogi suka halarci zaman kotun Kolin a yau.
Mai shari’a John Okoro dake jagorantar Alkalai tara,ya amince da shigar da manyan lauyoyin jihohin Katsina Legas da Ondo da Ogun da Ekiti da kuma Sokoto a matsayin masu shigar da kara.
Kotun ta umarci masu gabatar da kara na asali da wanda ake kara da sukakunshi Babban Lauyan Tarayya da su gyara sauran Karar ta farko domin sanya sabbin bangarorin.