A Ranar Alhamis ne Kotun kolin Amurka ta yanke hukuncin cewa, Amurkawa na da yanci na rike bindiga a biyanar jama’a, Wannan hukunci na zuwa ne makonni bayan wani kazamin harin bindiga da aka kai a makaranta.
Hukuncin ya ci karo da dokar da birnin New York ya saka, wanda ke bukatar mutum ya yi cikakken bayani akan cewar yana da yancin mallakar bindiga domin kare kansa, kafin samun lasisin mallakar bindigar.
Duk da kiraye-kirayen da ake ta yi na kayyade amfani da bindigogi bayan jerin harin bindiga biyu da aka samu a watan Mayu, kotun ta goyi bayan masu fafutuka da suka ce kundin tsarin mulkin Amurka ya ba da damar mallakar bindigogi da kuma daukar makamai.
Hukuncin shine na farko da kotu ta yanke a cikin shekaru goma da aka kwashe ana dambarwa kan amfani da makami a kasar.