Jam’iyyun APC da PDP a jihar Osun sun baiyana fatan samun nasara a yayin da Kotun Koli zata aiyana halastaccen wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka yi ranar 16 ga watan Yulin bara, A yau Talata.
Idan ba’a manta ba, A hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar ta yanke ranar 27 ga watan janairun bana, karkashin mai shari’a Tertse Kume, Ta soke nasarar da gwamna Adeleke na jam’iyyar PDP ya samu tare da aiyan tsohon gwamnan jihar Oyetola na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka yi.
Sai dai saboda rashin gamsuwa da hukuncin ne, Gwamna Adeleke tare da jam’iyyarsa ta PDP, garzayawa gaban kotun daukaka kara, Wanda a ranar 24 ga watan Maris din bana ne kotun ta soke hukuncin da kotun baya ta yanke,Tare da sake tabbatar da Adeleke a matsayin wanda ya samu nasara.
A mabanbantan hirar da suka yi da manema Labarai gabanin hukuncin na yau da za’a yanke, kakakin jam’iyyar APC a jihar Kola Olabisi, da kuma takwaransa na jam’iyyar PDP Oladele Olabamiji, Kowannensu ya baiyana fatan cewar tsaginsu ne zai samu nasara.