Kotun kolin Najeriya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta tabbatar da Alhaji Abba Kabir Yusuf a matsayin zababben gwamnan jihar Kano.
Jam'iyyar APC ta kalubalanci Nasarar Abba Kabir a Zaben Gwamna a 2023 da dan takararta na Gwamna a Kano, Nasiru Yusuf Gawuna.
Hukuncin da aka yanke a yau Juma’a ya biyo bayan shafe watanni ana shari'a daga Kotun kararrakim zabe zuwa Kotun daukaka kara da kuma Kotun Koli tsakanin jam’iyyar NNPP da APC a jihar ta Kano.
Tuni aka tsaurara matakan staro a Jihar gabanin hukuncin.