Kotun Koli ta amincewa gwamnatin taraiyya shigar da wasu sabbin tuhume-tuhume guda tara akan karar data daukaka zuwa gaban kotun, inda take kalubalantar hukuncin da wata kotu ta yi na bada umarnin sakin jagoran kungiyar masu fafutikar kafa kasar Biyafara, IPOB, Nnamdi Kanu.
Gwamnatin taraiyya ta hannun lauyanta, Tijjani Gadzali, ta nemi kotun ta bada izinin shigar da sabbin tuhume-tuhumen da aka yiwa gyara, cikin kunshin karar data shigar gabanta a ranar 28 ga watan Oktoban 2022.
Kotun kolin karkashin alkalai biyar bisa jagorancin John Okoro, Sune suka baiwa gwamnatin taraiyyar damar a ranar Alhamis.
A wani bangaren kuma, A yayin zaman shari’ar ta Jagoran kungiyar IPOB Nmadi Kanu, Lauyansa Mike Ozekhome, Ya fadawa alkalan kotun kolin cewar, Daga cikin dalilan da suke son a bada belin Nmadi Kanu hadda magana ta rashin lafiya da yake fama da ita.
Lauyan ya nemin kotun da kodai ta bada belin Nnamdi Kanu ko kuma ta sake aikewa da shi gidan Ajiya da gyaran hali na Kuje,har zuwa lokacin da za’a kammala zaman shari’ar da ake masa.
To sai dai a sukar da ya gabatar, Mai gabatar da kara ya baiyana cewar wurin da hukumar tsaro ta farin kaya DSS ke tsare da Nnamdi Kanu mai inganci ne, kuma an tanadi duk wani abu da ya dace da kula da lafiyarsa.
Bayan sauraren bukatar ne, Kotun kolin ta shawarci Lauya Ozekhome dake kare Nnamdi kanu da ya janye bukatun nasa domin samun saurin gudanar da shari’ar.