Kotun Koli ta yanke hukuncin cewa, Dole ne Dan takarar sanatan Kano ta tsakiya a karkashin jam’iyyar APC, Abdulsalam Abdulkarim, wanda aka fi sani da A.A Zaura, ya baiyana gaban babbar kotun taraiyya dake zamanta a nan Kano, domin fuskantar tuhume-tuhumen da hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ke yi masa.
Kotun ta yanken hukuncin ne, bayan lauyan A.A Zaura Barrister I.G Waru ya shigar da karar, Sannan kuma ta yi fatali da bukatar da Dan takarar sanatan KANO ta tsakiya, AA zaura ya shigar gabanta, na neman a hana babbar kotun taraiyyar cigaba da yi masa shari’a.
Idan ba’a manta ba, Hukumar EFCC na tuhumar A.A Zaura da damfarar wani dan kasar Kuwaita tsabar kudi dala milyan 1 da dubu 300 da dubu 20, ta hanyar baiyana kansa, a matsayin dan kasuwar dake harkokin gine-gine a Dubai da Kuwait da sauran wadansu kasashen Larabawa .