On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Kotun Koli Ta Sake Tabbatar Da Ademola A Matsayin Gwamnan Jihar OSun

Ademola

Kotun Koli ta tabbatar da nasarar da gwamnan Jihar Osun Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP ya samu, a zaben gwamnan Jihar da aka yi bara.

 A hukunci da Mai sharia Emmanuel Agim, ya karanta na hukuncin da kotun ta yanke, Ya sake jaddada hukuncin da kotun daukaka kara ta zartar na tabbatar da samun nasarar da Gwamna Ademola Adeleke ya samu.

Idan ba'a manta ba, Tsohon gwamnan Jihar Osun Oyetola da jam'iyyar sa ta APC sun garzaya gaban kotun Koli, suna bukatar ta jingine hukuncin da reshen kotun daukaka kara Mai zamanta a Abuja ta yanke, Wanda ya soke hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan Jihar ta zartar na tabbatar Oyetola a matsayin Wanda ya lashe zaben gwamnan da aka yi ranar 16 ga watan Nuwambar 2022.