On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Kotun Kararrakin Zabe Zata Ayyana Obi Amatsayin Shugaban Najeriya - Abure

Shugaban wani tsagi na jam'iyyar Labour, Julius Abure, ya ce Kotu zata ayyana dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Peter Obi, amatsayin shugaban Najeriya.

Abure ya yi magana ne a lokacin da yake jawabi ga wasu ‘yan Najeriya a Amurka  a ziyarar da ya kai kasar.

Obi wanda ya zo na uku a zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Fabrairu shi da jam’iyyarsa na kalubalantar sakamakon zaben, inda ya nemi kotu ta soke nasarar shugaba Bola Tinubu, na  jam’iyyar APC.

Abure, wanda ke rangadi a Burtaniya da Amurka, ya ce hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa zai zo ne kafin ko ranar 16 ga watan Satumba.