Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta bukaci kungiyar malaman jami’o’I ta kasa ASUU da gwamnatin tarayya da su zabi yin sulhu a tsakaninsu batare da takaddamar dake tsakaninsu ta kaisu gaban kotu ba.
Kotun ta dauki wannan matsayin ne a yau yayin da take sauraron karar da kungiyar ASUU ta shigar kan hukuncin da kotun ma’aikata ta kasa ta yanke a ranar 21 ga watan Satumba, inda ta umarci malaman jami’o’in da su dakatar da yajin aikin da suke yi.
Jagoran lauyoyin ASUU, Femi Falana SAN da lauyan gwamnatin taraiyya James Igwe SAN, Sune ke jan ragamar shari’ar.
Idan ba’a manta ba kungiyar ta ASUU ta tsunduma yajin aikin ne tun daga ranar 14 ga watan Fabarairun bana, A yayin da cikin watan Augustan bana, kungiyar ta aiyana yajin aikin nata a matsayin na sai baba ta gani, bayan data baiyana cewa gwamnati ta gaza biya masu bukatunsu.
Kungiyar malaman jami’oi ta kasa ASUU, na neman a inganta masu kudaden inganta walwala, dana farfado da jami’oi da sauran wasu hakkoki wanda kudin ya kama kimanin naira tiriliyan 1 da bilyan 1.
To sai dai wani hanzari ba gudu ba, Gwamnatin taraiyya ta baiyana cewa bata wannan makudan kudi da kungiyar ke neman, inda ta danganta matsalar da saukar farashin danyen mai da ake samu a zamanin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.