An gurfanar da wasu matasa biyu, Mubarak Muhammad da Kuma Nazifi Bala a gaban wata kotun Majistare mai lamba 58 dake nan Kano, bisa zarginsu da bata sunan gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje.
A cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafin sada zumunta na facebook, Matasan biyu sun baiyana cewa gwamna Ganduje yana siyar da filayen mutane, sannan kuma yana yin Likimo, Matasan biyu sun amsa lefin da ake tuhumarsu das hi bayan da aka fara karanta masu abunda ake zarginsu da yi.
Daga nan ne kotun ta dage zamanta zuwa ranar 7 ga watan Nuwambar da muke ciki domin yanke masu hukunci.
Hukumar tace fina-finai da Dab'i ta jihar kano karkashin Afakallah ce ta gurfanar da matsan biyu gaban kotu.