On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Kotu Tayi Watsi Da Karar Dake Neman Soke Zaben Ademola Adeleke A Matsayin ‘Dan Takarar Gwamna Na Jam’iyyar PDP A Jihar Osun.

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta yi watsi da karar da ke neman soke zaben Ademola Adeleke a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP bisa dalilan da suka ce ya saba wa doka.

Alkalin kotun, Mai shari’a Obiora Egwuatu, ya yi fatali da karar a kan cewa wanda ya shigar da karar, Awoyemi Oluwatayo Lukman, ba shi da hujja daya dogara da ita wajen shigar da karar.

Alkalin ya  ce an kori karar ne, kasancewar kotun ba ta da hurumin sauraren karar.

Wanda ya shigar da karar, Awoyemi Oluwatayo Lukman, ya maka hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da Jam'iyyar PDP da Adeleke a gaban kotu, inda ya nemi kotu ta baiwa INEC umarnin soke sunan Adeleke a matsayin dan takarar PDP, sakamakon cewa bai cika ka'ida ba.