Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a nan Kano, ta yi mi’ara koma baya, akan wani umarnin wucin gadi data bayar a zamanta na baya, wanda ya hana yunkurin gwamnatin jihar Kano, na ciwo bashin tsabar kudi da suka kai naira biliyan 10.
Karar wadda aka shigar ta hannun babban daraktan gamayyar kungiyoyin farar hula,mai suna KFF, Dr Yusuf Isyaka Rabi'u, Ya bukaci kotun ta dakatar da gwamnatin jihar kano ciyo bashin makudan kudaden.
Tunda fari dai, kotun ta hana ciyo bashin, wanda gwamnatin tace zata yi amfani dasu ne wajen sanya kyamarorin tsaro na CCTV domin inganta sha'anin tsaro a jihar nan .
Alkalin kotun, mai shari'a Abdullahi Liman, ya janye umarnin wucin gadin daya bayar a ranar 1 ga watan Yuli, biyo bayan bukatar da Lauyan wadanda ake kara Muhammad Dahuru yayi, inda ya roki kotun data jingine hukuncinta na baya data yi.