A ranar 22 ga watan Satumbar bana ne, Kotu zata yanke hukunci kan karar da tsohon gwamnan jihar kano,Abdullahi Umar Ganduje ya shigar gabanta, na neman ta hana hukumar karbar korafe –korafe da yaki da cin hanci ta jihar Kano yin bincike akansa.
A jiya ne Lauyan hukumar, Femi Falana SAN,Ya baiyana cewar rigar kariyar da tsohon gwamnan ke amfani da ita tazo karshe a ranar 29 ga watan Mayun bana, A saboda haka babu wata kotu da zata iya kare shi ko iyalansa ko kuma wadanda ya yi aiki tare dasu daga wani bincike.
To sai dai a martanin da Lauyan Ganduje ya yi, Ya baiyana cewar ba’a ka’idar data kamata ba,sannan kuma an take masa hakkinsa na Dan adam.
Gwamnatin jihar kano mai ci a yanzu dai ta dauki matakin yin bincike kan wani faifan bidiyon Dala da ake zargin anga tsohon gwamnan kano Ganduje na karbar cin hancin Dala daga hannun wani Dan kwangila, Zargin da tsohon gwamnan ya musanta.