Wata babbar kotun jihar Ekiti da ke zamanta a birnin Ado Ekiti ta yanke wa wasu mutane uku hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samun su da laifin hada baki da kuma fashi da makami.
Wadanda aka yankewa hukuncin sun hada da Omotayo Deji da Chidiebere Ifeanyin da kuma Bolaji Usman, inda aka gurfanar da su a gaban mai shari’a Bamidele Omotoso a ranar 21 ga watan Janairun 2020, bisa tuhume tuhume hudu.
A bayanin da ya yi wa ‘yan sanda, Daya daga cikin mutanen da aka yiwa fashi da makamin, Ya ce mutanen sun afka masu da sara da adduna da sauran wasu makamai, inda suka karbe masu wayoyinsu na hannu da Na’ura mai kwakwalwa kirar tafi da gidanka, sai Caja da kum na’urar yin cajin waya.
A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Bamidele Omotoso, Ya yanke masu hukuncin kisa ta hanya.