Wata Babbar kotun taraiyya dake zamanta a Akwa Ibom, ta yankewa dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar YPP, Bassey Albert hukuncin zaman gidan gyaran hali na tsawon shekara 42, sakamakon aikata lefin Damfara.
A shekarar 2019 ne, Hukumar EFCC ta gurfanar da Albert gaban kotun bisa tuhumarsa da aikata lefuka shida, inda ta zarge shi da mallaka wasu motoci shida akan kudi naira milyan 204 a lokacin da yake kwamishinan kudi na jihar.
A hukuncin data yanke, Mai shari’a Agatha Okeke, ta samu dan takarar gwamnan kuma sanatan Akwa Ibom ta Arewa maso gabas da aikata lefukan, sannan kuma ta aike dashi zuwa gidan gyaran hali na Ikot Ekpene.
A baya Albert ya kasance dan jam’iyyar PDP kafin ya sauya sheka zuwa jam’iyyar YPP, inda ya samu tikitin takarar kujerar gwamnan jihar a zabe mai zuwa.