On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Kotu Ta Yankewa Hushpuppi Hukuncin Daurin Shekara 11 A Kasar Amurka

Wata kotun Amurka dake California ta yankewa Ramon Abass wanda aka fi sani da Hushpuppi hukuncin daurin shekara 11 da watanni uku a gidan yari bisa samunsa da laifin hada baki da damfara hanyoyi daban-daban a yanar gizo.

Mai shari’a Otis Wright na II shi ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin, kuma an samu Hushpuppi da laifin zarge-zargen da suka hada da damfara ta hanyar shirin tallafin da kudin karatu da wasu tsare-tsare email na kasuwanci da sauran tsare-tsare na yanar gizo na yaudara.

Kotun ta kuma umarci Hushpuppito ya biya dala milliyan 1 da dubu dari 7 ga wadanda ya damfara.

Idan za’a iya tunawa matashin mai shekara 37 ya amsa dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa.

Wannan hukuncin shine ƙarshen shari'ar Hushpuppi tun lokacin da aka kama shi a watan Yuni na shekarar 2020 a wani otal dake birnin Dubai.